Wani Dan shekara 38 ya gamu da ajalinsa bayan da tsawa ta fado masa a yankin Mura-Lopit na Gabashin Equatoria a ranar litinin dake Lafon.
Rahotanni sun bayyana cewa, Mamacin wanda aka ambata da suna James yana tare da wasu mutane uku wanda su ka samu raunuka, Mutanen suna zuwa kamun kifi a rafin Midihir kafin ruwan sama mai karfi ya fara sauka daga bisani Aradu ta afka a kan su.
A cewar wani Mazaunin yankin da ya bayyana cewa, biyu daga cikin mutanen da lamarin ya so ritsawa da su, sun yi nasarar komawa gida inda su ka kai rahoton afkuwar lamarin.
Sai dai dangane da al’adar mutanan yankin, Idan a ka ce tsawa ta fada kan mutum to a kwai dalili ko kuma Ana zaton mutum la’ananne ne. Kamar yadda Mazaunan yankin suka shaida mana.