fbpx
Thursday, March 4
Shadow

Tsawaita wa’adin Shugaban yan sanda, Adamu babbar alheri ne ga jihar Nasarawa>>Gwamna Sule

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce karin wa’adin da aka baiwa Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP, Muhammad Adamu babban alheri ne ga jihar.
Gwamnan ya nuna jin dadinsa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda karin wa’adin watanni uku ga IGP.
Sule ya fadi haka ne yayin taron da ya hada da masu ruwa da tsaki daga Awe, Tunga da Ribi, dukkansu a karamar hukumar Awe ta jihar, da kuma manyan ma’aikatan kamfanin sikari ta Dangote a ranar Litinin a Lafia.
Yayin da yake godewa Allah kan dukkan ni’imomin da ke zuwa jihar, gwamnan ya yi godiya ta musamman ga Shugaban kasa kan tsawaita wa’adin IGP, dan Nasarawa.
Sule ya kasance cikin farin ciki musamman a lokacin da wasu shugabannin hukumomin tsaro ke tafiya, Shugaban kasar ya ga Adamu ya cancanci a kara masa wa’adi.
Gwamnan ya kuma yi amfani da damar taron don yaba wa IGP saboda kasancewarsa kyakkyawan jakadan jihar da kuma kyakkyawan jagoranci da ya ba shi damar tabbatar da tsawaita wa’adin.
A cewar Sule, aikin da IGP ya samu alheri ne ga jihar da jama’arta, saboda haka yabawa Shugaban kasar da wannan karimcin.
“Ina ganin wannan babbar ni’ima ce da ta same mu kuma ya kamata mu yi godiya ga hakan kuma mu gode wa Allah Madaukakin Sarki,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *