Tsohon gwamnan jihar Ekiti Adeyole Fayose ya kori babban mataimakinsa Sunday Anifowose saboda ya zabi Atiku a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.
Atiku Abubakar yayi nasarar lashe zaben fidda gwanin ne a ranar sati inda ya doke ‘yan takara 12 na PDP yayi nasarar samun tikitin shugaban kasa.
Inda yanzu zai tsayawa PDP a matsayin dan takararta kamar yadda ya tsaya mata a zaben shekarar 2023.