fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tsohon mai rikon mukamin shugaban hukumar zabe na kasa farfesa Maurice Iwu ya samar da maganin cutar Covid-19 wanda a halin yanzu kasar Amurka ke gudanar da bincike akai domin tabbatar da shi

Farfesa Maurice Iwu dan Najeriya wanda ya shiga jerin masu yun kurin samar da maganin cutar Coronavirus wanda ta lakume dubban jama’a a fadin duniya

Farfesa Maurice Iwu farfesa ne a fanni sanin ilimin magun guna ta hanyar tsirai, wanda ya ke a Jami’ar Nigeria Nsukka (UNN).

Farfesa Maurice Iwu ya bayyana samar da maganin ta hanyar tsirrai inda ya ce a yanzu maganin yana can kasar amurka wanda ake gudanar da gwajin sa, inda ya bayyana dazarar an tabbatar dashi za a fara amfani da maganin.

Karanta wannan  Hotuna: Kungiyar kiwon lafiya ta kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa

Maganin wanda aka gabatarwa da ministan kimiyya da fasaha Ogbonnaya Onu wanda kuma ministan ya aike da irin maganin kasar Amurka domin gudanar da gwaji don tabbatar dashi.

Farfesa Maurice Iwu sananne ne wanda ya taba rike mukamin shugaban hukumar zabe na kasa a shekarar 2005, a zamanin mulkin Obasanjo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.