Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Omisore ya sauya shekar ne a Mazabarsa dake a Ile-Ife, A Jihar Osun, bayan haka, ya karbi katin zama mamban jam’iyyar.
Tsohon Mataimakin Gwamnan ya tsaya takarar Gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar Social Democratic Party, SDP.