fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya goyi bayan Gwamna Ganduje kan dakatar da Sheikh Abduljabbar daga yin wa’azi a Jihar

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya yaba wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje kan hana fitaccen malamin nan, Sheikh Abdujjabar Nasiru-Kabara yin wa’azi a jihar.

A ranar laraba da ta gaba ne, Gwamna Ganduje ya hana Malam Abduljabbar Nasiru-Kabara yin wa’azi a jihar, inda ya bada umarnin rufe masallacin sa, wanda ke karamar hukumar Gwale a cikin garin Kano.

An bayar da umarnin ne biyo bayan korafe-korafen da ake yi cewa mai wa’azin yana zagin sahabban Annabi Muhammad (S.A.W) a cikin tafsirinsa na addini.

Tsohon Sarkin ya yi wannan yabo ne lokacin da yake gabatar da lacca daga Oxford, UK, yana mai cewa shawarar da gwamnatin jihar ta yi na hana Mista Nasiru-Kabara abin a yaba ne kuma ya kamata a goyi bayansa.

Karanta wannan  Dandazon Mata Sun Yi Bikin Kona Tsintsiyar Jam'iyyar APC A Kaduna

A cewarsa, Musulmai a Kano masu bin tafarkin “Ahlussuna wal Jama’a” ne kuma a shirye suke su yi watsi da duk wanda zai kawo wasu sabbin abubuwa ga addinin Musulunci a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.