fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Tsohon shugaban Amirka Barack Oabama ya yi kakkausar suka kan yadda Trump ke yaki da Coronavirus

Tsohon shugaban Amirka Barack Oabama ya yi kakkausar suka ga yadda shugaba Trump yake tafiyar da yaki da annobar corona.

 

Obama yace matakan da Trump ke dauka suna cike da tabargaza da rashin tsari. Ya yi wadannan kalaman ne a lokacin da yake tattaunawa da wasu tsoffin jami’an gwamnatinsa.

Mutane fiye da 77,000 suka rasu a Amirka a sakamakon annobar ta coronavirus yayin da adadin wadanda suka kamu da kwayar cutar a Amirka ya haura mutum miliyan daya da dubu dari uku.

 

A halin da ake ciki dai wasu jihohin Amirkar na shirin fara bude harkokin yau da kullum yayin da jami’an lafiya ke sa ido game da yiwuwar sake barkewar annobar a karo na biyu.

A waje guda kuma kasashen China da Koriya ta Kudu sun ruwaito karuwar sabbin kamun cutar ta Coronavirus a yau Lahadi, abin da ya tada hankali a kasashen da annobar ta yi sauki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.