Abba kyari: Tsohon Shugaban kasa goodluck Jonathan ya jajantawa iyalan Abba kyari
Tun bayan bayyanar mutuwar shugaban ma’aikata manyan mu karraban gwamnati dake fadin Najeriya ke ta aikewa da sakon ta’aziyyar su ga Iyalan Abba kyari.
Dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar shima ya aike da sakon ta’aziyyarsa
Gwamnoni yan siyasa yan kasuwa duka suna ta aikewa da sakon jajantawa ga iyalan Abba’kyari.
Tsohon shugaban kasa goodluck, yayi ta’aziyar rashin shugaban ma’aikatan, inda ya rubuta a shafinsa na sada zumunci.
I condole with H.E @MBuhari, the Kyari family & all sympathisers on the demise of Mallam Abba Kyari who until his death was the Chief of Staff to the President of Nigeria.
May Allah grant him Al Jannah Firdaus & strengthen his family & friends during this moment of grief.
GEJ— Goodluck E. Jonathan (@GEJonathan) April 18, 2020
Inda ya bayyana tausayawa tare da jajantawa iyalan sa.
Kafun mutuwarsa Abba kyari ya kasance shine shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasar tarrayyar Najeriya.