A ci gaba da shari’ar da akewa tsohon Ministan ayyuka na musamman da dangantaka tsakanin gwamnatoci da kuma kula da ayyukan ma’aikatar kwadago na lokacin Tsohon shugaban kasa,Goodluck Jonathan, Tanimu Tukari(SAN) wani shaida yace Miliyan 200 ya bashi a yi taro kan tsaro, yayin da takardu suka nuna cewa Miliyan 359 tsohon shugaban kasar ya bayar akan aikin.
EFCC ta gurfanar da Tanimu Turaki a kotu tana tuhumarshi da almundahanar Miliyan 854. Tanimu ya rike mukamin Ministan tun daga shekarar 2013 zuwa 2015.
Da yake bada shaida a gaban kotu,tsohon me baiwa tsohon shugaban kasar Shawara akan harkokin Addinin Musulunci, Mr. Umar Tahir wanda shima lauyane yace ya baiwa tsohon shugaban kasar shawara kan a gudanar da taron wanda kuma ya amince.
Yace an hadashi da Minista Tanimu Turaki wanda ya bashi Miliyan 200 da aka rika bashi da Miliyan 50-50 wadda Miliyan 50 ta karshe a hannu aka bashi ita. Yace a yanzu ne ma da EFCC suka sameshi yake ganin cewa ashe Miliyan 359 aka amince a yi aikin dasu.
Mai Shari’a Iyang Ekwo ya daga ci gaba da Shari’ar zuwa 21 ga watan Satumba.