Tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Azubuike Ihejirika me murabus ya bayyana komawa jam’iyyar APC.
Hakan na zuwane bayan ganawar da yayi da Sanara Orji Uzor Kalu.
Yayi Rijistar Komawa APC a mahaifarsa dake Isuikwuato. Shine ya rike mukamin shugaban sojojin Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2014.