A ci gaba da bayar da tallafin Dubu 20 na gwamnatin tarayya, wajilan gwamnatin sun je garin Ajura, karamar hukumar Jahun, jihar Jigawa.
A garinne wata tsohuwa da ta ji an kira sunanta cikin wanda zasu amfana da tallafin kudin na gwamnatin tarayya ta fashe da kuka.
Rahoton yace saboda tsabar shauki ko kudin kasa rikewa ta yi saida jami’an dake rabon suka jata gefe suka zaunar da ita.
Bayan ta dawo cikin hayyacinta, Dailytrust ta zanta da ita inda ta bayyana cewa bata taba samun dubu 20 a dunkule ba, tace danta dake kula da ita ya rasu, jikokinta ne yanzu suke rike da ita kuma suma ba masu karfi bane.
Tace bayan mutuwar mijinta ita kadaice ta rainin yaranta har suka girma.