Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, tsufa na hanashi cimma burikan da ya saka a gaba a gwamnatinsa.
Shugaban ya bayyana cewa, sa’anninsa yawanci suna can suna hutawa.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a NTA ranar Alhamis.
Shugabab ya bayyana cewa ya kagara ya ga watanni 17 da suka rage masa sun yi ya sauka ya huta.
Yace kusan kullun sai yayi aikin awa 8 ana ta kawo masa takardu daga jihohi daban-daban, yace amma fa shine yace zai iya dan haka ba zai yi korafi ba.
Shugaba Buhari yace ya yi Gwamna, yayi Minista sannan gashi ya zama shugaban kasa karo na biyu dan haka yagi iya bakin kokarinsa.