Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa tubabbun ‘yan bindigar jihar sun kwato mutane 12 daga hannun masu garkuwa da mutane inda suka mikasu hannun ‘yansanda.
Me magana da yawun ‘yansandan jihar, SP Muhamnad Shehu ne ya tabbatarwa manema labarai haka inda yace tubabbun ‘yan bindigar sun kaiwa masu garkuwa da mutanen harin kwatan bauna inda suka kwato mutane 12 dake hannunsu.
Yace mutanen da aka kwato din an sacesune kimanin kamwanni 2 da suka gabata.
Kwamishinan ‘yansandan jihar,Usman Nagogo ya bayyana cewa an kubutar da mutanenne saboda alkawarin da tubabbun ‘yan bindigar suka cika na yakar abokansu da basu tubaba.
Ya jinjina musu da kuma alkawarin ci gaba da basu hadin kai.