fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Tun muna yara ake ce mana Buhari me gaskiyane:Bashi da laifi a gurin mu>>Rarara

Tauraron mawakin Siyasa wanda ya kware wajan yiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari wakar Yabo, Dauka Kahutu Rarara ya bayyana cewa su a gurinsu Shugaban kasar bashi da laifi.

 

Ya bayyana hakane a wata tattaunawa ta musamman da Kannywood exclusive suka yi dashi inda aka tambayeshi cewa ‘yan Najeriya basu taba jin ya fadi laifin shugaban kasa ba.

Sai ya kada baki yace ai su a gurinsu shugaba Buhari bashi da laifi. Yace indai a cikin sauaran ‘yan siyasa ne musamman wanda suka gabata to shugana Buhari ba zai yi laifi ba.

 

Yace bece shugaban kasar ma’asumi bane amma idan za’a kwatantashi da sauran ‘yan siyasa to za’a ga bashi da laifi.

 

Da aka masa maganar tsadar Rayuwa, Rarara yace wannan duk Duniya ne kowace kasa ta tabu yace a lokacin da APC ta zo ta iske Najeriya raga-raga a kasa saida ta yi kokari ta tayar da ita, yace har ana nunata ana samun a bada kudi a gyara can a gyara nan.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Firaym Ministan kasar Landan yayi murabus

Rarara yace a lokacin PDP mai saida ya kai dala 120 amma a yanzu 30 yake wani lokacin a samu yakai arba’in ya fado. Da yake magana akan harkar tsaro Rarara yace wannan kowa yana da rawar da zai taka dan sai an samu hadin kan wanda suke zaune a wajan sannan za’a samu tsaro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.