Matar mutuminnan na Kano da yayi batanci ga ma’aikin Allah, Annabi Muhammad(SAW) watau Mubarak Bala tace tunda aka daureshe ta kasa bacci ta kasa cin abinci.
Kotu ta daure Mubarak Bala tsawon shekaru 24 bayan da ya amsa laifinsa na cewa lallai yayi batanci ga Annabi(SAW).
Matar tasa Amina a yayin ganawa da manema labarai tace ta shiga halin damuwa tun bayan da ta ji hukuncin da aka yankewa mijin nata.
Tace hukuncin ya girgiza ta kuma duk sanda ta kulle ido Mubarak take gani dan hakane ma ta kasa bacci.
Tace an kama Mubarak ko shekara daya basu cika da yin aure ba inda tace a shekarar 2019 ne suka yi aure, ta kara da cewa, a lokacin, dansu satinsa 6 a Duniya, gashi yanzu zai tashi babu mahaifi.