fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Tunda an baka Khalifan Tijjaniyya, yanzu kana da damar hana Bara da Almajirci>>’Yan Arewa ga Sarki Sanusi

A jiya ne dai aka samu Rahotannin cewa an nada tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniyya na Najeriya.

 

Bayan Nadin, Wasu ‘yan Arewa sun hau shafukan sada zumunta inda suka rika kira a gareshi da yayi kokarin ganin an hana Almajirci da kuma bara.

 

Sun rika tuna masa cewa, a baya ya sha kira da a daina Bara da almajiranci, to yanzu ga dama ta samu a gareshi da zai yi a aikace.

 

Wani me suna Abubakar Hadimi ya bayyana cewa, shugabancin Tijjaniyya da Sarki Sanusi ya samu, damace Allah ya bashi ta kawo karshen Almajiranci a aikace. Ya bayyana cewa, kusan duka Almajirai ko dai ‘yan Qadiriyya ko Tijjaniyya ne. Yace yana fatan zai kira iyayen wadanna yara dan su kwashesu daga kan tituna.

 

Ya kara da cewa, ci gaba da magana ba tare da daukar mataki a aikace ba, ba zai bayar da sakamakon da ake so ba.

 

With the Tijjaniyya leadership now enthroned on Sanusi Lamiɗo, God Has given him another opportunity to end ALMAJIRANCI PRACTICALLY. Almost all Almajiris are either of the Tijjaniyya or Qadiriyya clan. We hope he calls them all back home, & ask them to take their children back.

 

It will be counter productive to see him or hear him now continue with the same approach of too much noise & no action which he is very popular with. A while Khalifa can act now, and not make too much noise.

 

Shima wani me suna, Njidda Abdulrauf ya bayyana cewa, Sarki Sanusi yayi ta kiraye-kirayen a daina Bara da Almajirci, to yanzu ya samu Iko, bari mu gani.

 

He was the one agitating for almajiri theoritically so now he has the power …let see

Karanta wannan  Gwamna El Rufa'i yayi fashin baki kan sauyawa jihar Kaduna suna

 

Saidai wani me suna, Ali Biu ya bayyana cewa, Abubakar yayi magana me kyau saidai be kamata ya dora maganar akan Almajirci akan wata kungiya ba. Yace dan haka sai yayi kira ga Ahlussunnah su kawo karshen Boko Haram tunda Shekau yana ikirarin shima dan kungiyar ne.

 

 

You made a valid point however, blaming the whole Almajiri system on a group is a petty move, which is not surprising coming from you. As you are at it, you can also call out the “Ahlul Sunnah” leaders to end Bokoharam since Shekau has been claiming affiliation to the group.

 

 

the Appointment Of Alhaji Sunusi Lamido Sunusi as Khalifahn Tijjaniyyar Nigeria presents a Golden opportunity for Banning the Almajiri System In the North as he has been the most vocal about the issue, if he fails to do so, then we will know where to categorize him.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.