Wasu Inyamuraibsun fara bayyana ra’ayinsu kan wanda zai zama shugaban kasa a 2023.
A yayin da ake tunanin a 2023 dan kudu ne zai zama shugaban kasa, saidai ana takun saka tsakanin yarbawa da Inyamurai kan wanda ya dace yayi shugabancin kasar.
Tinubu da Osinbajo ne suka fito a yankin Yarbawa yayin da a yankin Inyamurai kuwa akwai ‘yan takara da yawa.
Saidai wasu Inyamuran musamman a shafukan sada zumunta sun bayyana cewa Yarbawa sun yi shugaban kasa sun kuma samu mataimakin shugaban kasa amma sun kasa bar musu a wannan karin suma su samu mukami.
Karanta wannan Masu adaidaita sahu sunyi zanga a jihar Adamawa kan kwace masu kekuna da kudin haraji
Suke cewa dan haka gara kawai dan Arewa ya sake samun shugaban kasar a 2023 kowa ya rasa dadai su zabi bayerabe.