fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Tunda Muka taso muke jin ana cewa Buhari me gaskiya, Kun kara jin ana cewa wani me gaskiya Duk Najeriya?>>Rarara

Tauraron mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa tun suna kananan yara ake cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari me gaskiya kuma har yanzu ana fada.

 

Rarara ya bayyana hakane a hira ta musamman da Kannywood exclusive suka yi dashi kan akan sabuwar wakar da zaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari wadda yace talakawane zasu biya kudin yin wakar.

Rarara yace yana da niyyar tattaro duka ayyukan da shugaban kasar yayi daga kudu da Arewa dan bayyanasu a cikin wakar tasa, saboda wasu basu san dasu ba.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Firaym Ministan kasar Landan yayi murabus

 

Da yake magana akan Nagartar shugaban kasar, Rarara yace tunda suna yara ake cewa shugaba Buhari mai Gaskiya kuma har yanzu ana fada.

Ya tambayi wadda ke masa tambayoyi cewa shin duk Najeriya ta kara ji ance ga wani me gaskiya?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.