fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Tunda shugaba Buhari ya zama shugaban kasa ko fentin gidansa na Kaduna ba’a canja ba>>Inji Hadiminsa

Hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari watau Bashir Ahmad ya bayyana cewa, tun da shugaban kasar ya ci zabe ba’a canja komai a gidansa na Kaduna ba.

 

Shugaba Buhari yayi ziyarar kwanaki 2 a jihar Kaduna. Inda bayan kammala ziyarar ya je gidansa na Kadunan.

 

Wani ya bayyana cewa da alama babu abinda aka canja a gidan shugaba Buhari bayan da ya zama shugaban kasa ko fenti ma.

 

Bashir Ahmad ya tabbatar da cewa lallai wannan magana haka take.

Hakanan a wani jawabi me kama da wannan kuma, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kammala ziyarar da yake a Kaduna inda ya koma Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published.