fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tura ta kai Bango: Za’a dawo da sojojin da suka yi ritaya dan su taimaka a kawo karshen matsalar tsaro

Shugaban sojojin Najeriya, Janar Farook Yahya ya bayyana cewa, za’a dawo da sojojin da suka yi ritaya dan su taimaka a kawo karshen matsalar tsaron da ake fama da ita.

 

Ya bayyana cewa tuni suka fara shirin hakan dan ganin an zakulo wanda suka cancanta an kuma dawo dasu bakin aiki dan taimakawa a kawo karshen matsalar tsaron da ake fama da ita a Arewa maso Gabas.

Ya kuma yi kira ga sojojin da suka ajiye aikin da su ci gaba da taimakawa wajan magance matsalar tsaron da ake fama da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published.