fbpx
Thursday, June 30
Shadow

TURKASHI: Budurwa Ta Maka Mahaifinta A Kotu A Jihar Kaduna Saboda Ya Hana Ta Auren Wanda Take So

Daga Sani Musa Mairiga

Tirkashi, so hana ganin laifi! Wata budurwa mai karancin shekaru mai suna Halima Yunusa ta maka mahaifinta a kotun shari’ar musulunci dake Magajin Gari a jihar Kaduna, saboda wai ya hana ta auren wanda take matukar so, wato Bashir Yusuf Yunusa wanda ke zaune a Kasuwar Magani dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Ta shedewa kotun cewa tana matukar kaunar Bashir amma iyayenta sun ce faufau ba za su taba yarda ta aure shi ba. Shine dalilin da ya sa ta yi karar mahaifin nata.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya ta bayyana farashin da za'a sayar da litar mai tace zata hukunta gidajen man dake sayar da litar fetur naira 180

Malam Ibrahim wanda shine mahaifin budurwar ya shedewa kotun cewa yana sane da soyayyar dake tsakanin ‘yar sa da saurayin wanda har ya umurce shi da ya turo iyayen sa su kawo sadaki amma shuru kake ji yau kusan shekara daya kenan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.