Wednesday, June 3
Shadow

Unai Emery ya bayyana sunan dan wasan da zai maye gurbin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi

Tsohon shugaban Arsenal da PSG Unai Emery ya bayyana sunan tauraron da zai maye gurbin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi a matsayin zakaran wasannin kwallon kafa na duniya.

Messi da Ronaldo sun mamaye duniyar wasan kwallon kafa fiye da shekaru goma da suka gabata kuma sun lashe kyaututtukan balloon d’Or har sau 11 tsakanin su.
Amma yanzu zakarun sun fara fuskantar shekaru su na karshe a wasannin kwallon kafa yayin da shi kuma Emery ya bayyana dan wasan daya horar a kungiyar PSG a matsayin zakaran da zai maye gurbin Ronaldo da Messi.
Kuma dan wasan shine tauraron Brazil wato Neymar, wanda yayi aiki tare da Emery a kungiyar Paris saint German bayan sun siyo shi daga Barcelona a farashin da ba’a taba siyan wani dan wasa ba, euros miliyan 198 a shekara ta 2017. Emery ya gayawa Marca cewa Neymar kwararren dan wasan ne kuma yana da damar zama zakaran yan wasan kwallon kafa.
Ronaldo ya girmi Neymar da shekaru Bakwai yayin da shi kuma Messi ya girmi shi da shekaru 4. Neymar ya samu nasarori har guda 7 a lokacin daya ke buga wasa a kungiyar Barcelona, yanzu a PSG kuma ya lashe gasar lig 1 har sau uku a jere bayan a baiwa PSG kofin lig 1 saboda an dakatar da wasannin kwallon kafa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *