fbpx
Thursday, June 30
Shadow

UniAbuja ta kori farfesoshi biyu bisa zargin yin lalata da dalibai mata domin basu sakamakon jarabawa mai kyau

Hukumar gudanarwar jami’ar Abuja (UniAbuja) ta kori malaman jami’ar (Farfesoshi) biyu bisa zargin cin zarafin dalibai mata domin su basu sakamakon jarabawa mai kyau.

Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Abdul-Rasheed Na-Allah ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na NAN a birnin New York na kasar Amurka a ranar Litinin 6 ga watan Yuni, 2022.

A cewarsa, jami’ar ta bullo da wata manufa ta cin zarafin mata a harabar jami’ar, inda ta ce an wallafa manufar.

Na-Allah, wanda ya kai ziyarar kwanaki biyu a kasar Amurka, domin ganawa da kungiyar tsofaffin daliban Jami’ar Abuja, reshen Amurka, domin neman tallafi ga wannan makaranta, ya bayyana cewa akwai bukatar a ba wa dalibai mata a jami’ar kariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.