fbpx
Thursday, December 7
Shadow

Uwargidan Alex Ferguson ta mutu

Cathy Ferguson, matar tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson, ta rasu tana da shekaru 84 a duniya.

Mutanen biyu sun yi aure ne a shekara ta 1966, inda suka shafe shekaru 57 a matsayin mata da miji, kuma sun haifi ƴaƴa maza uku, ciki har da kocin Peterborough Darren Ferguson.

An sauke tutoci a Old Trafford a matsayin alamar girmamawa, kuma ƴan wasan ƙungiyar maza da mata za su daura bakaken ƙyalle a hannunsu a wasanninsu da za su buga a karshen wannan makon.

Manchester United a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: “Kowa a Manchester United yana mika sakon ta’aziyyarmu ga Sir Alex Ferguson da iyalansa bisa rasuwar Lady Cathy, uwa, ƴar’uwa, kuma kaka, kuma wadda ta kasance ginshiƙi mai karfi ga Sir Alex a duk tsawon rayuwarsa.”

Cathy da Sir Alex, mai shekaru 81, sun hadu ne a shekara ta 1964 yayin da dukkansu ke aiki a masana’antar kera keken rubutu.

Sir Alex ya kasance kocin Manchester United na tsawon shekaru 27 da suka yi tare kuma an ce Cathy ta taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan shi kada ya yi ritaya a shekara ta 2002.

Lokacin da Sir Alex ya sanar da yin ritaya bayan shekaru 11, ya ce: “matata Cathy ta kasance babban jigo a tsawon rayuwata.”

Kungiyoyi da dama sun aike da sakonnin girmamawa da ta’aziyya a shafukansu na sada zumunta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *