fbpx
Monday, December 5
Shadow

Uwargidan shugaban kasa Haj. A’isha Buhari ta dauki nauyin koyar da matasa sana’o’in hannu a Kano

Uwargidan shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari karkashin gidauniyarta me suna Future Assured da take tallafawa yara, mata da matasa dan su dogara da kansu ta dauki nauyin wasu matasa a jihar Kano inda aka koya musu sana’o’i irir-iri wanda zasu hanasu zaman banza harma su taimakawa ‘yan uwansu.

Horaswar wadda akayita tsakanin ranekun 31 da watan Octoba zuwa 3 ga watan Nuwamba ta koyar da matasa ayyukan hannu irinsu yin fenti, aski, sarrafa fata dadai sauransu, yanzu haka an yaye daliban kuma wasu daga cikinsu kamar yanda rahotanni suka nuna sunyi godiya da irin wannan tallafi da suka samu.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *