fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari tayi kira da’a sake duba dokar yiwa masu cin zarafi hukunci

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari karkashin gidauniyarta me suna Future Assured ta shirya wani taron bita akan cin zarafi da akewa musamman mata, kananan yara, da sauran mutane.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Uwargidan shugaban kasar tayi kira ga masu ruwa da tsaki a fannin shari’a dasu sake duba dokar dake ladabtar da masu cin zarafi, inda tayi misali da wani mutum a jihar Kano da yayi lalata da wata karamar yarinya ‘yar shekaru shida da haihuwa amma aka mai tarar naira dubu goma kawai. Uwargidan tayi kira ga duk wani wanda aka yiwa cin zarafi ta kowane irin fannine ya fito ya fada, dan a kwatarmai ‘yancinshi.
Har ta bayar da imel adress inda tace duk wani wanda akawa cin zarafi zai iya aike da sako ta cikin imel din dan a kawomai dauki, imel din shine, futureassured.org.ng
Ministan shari’a Abubakar Malami da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo sun halarci gurin taron inda duka sukayi Allah wadai ta cin zarafi da ake samu da kuma duk wanda aka yiwa ya fito ya bayyana dan abi mishi hakkinshi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *