fbpx
Monday, December 5
Shadow

Uwargidan Shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari ta kaddamar da ofishin gidauniyarta ta Future Assured a Kano

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta bude ofishin gidauniyarta ta Future Assured reshen jihar Kano a ziyarar data kai jihar yau Litinin, haka kuma ta shaida yaye matasa dari biyar da aka horas a fannin sana’o’i daban-daban karkashin gidauniyartata.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Hajiya A’isha Buhari tayi kira ga matasan da suka samu wannan horaswa da suyi amfani da wannan dana wajan dogaro da kanau harma su samawa wasu aikinyi a karkashinsu. Itama uwargida gwamnan jihar Kano, Dr. Hafsat Umar Ganduje ta godewa uwargidan shugaban kasar da mijinta saboda irin abubuwan Alherin da sukewa jihar ta Kano.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya halarci gurin yaye matasan inda shima yayi kira ga a kara fadada irin wannan horaswa zuwa ga ma’aikatan gwamnati da kuma malaman addinin musulunci dan suma suci gajiyar abin. Kuma yace irin wannan zai taimaka wajan kawar da hankalin matasa akan shaye-shaye.

Uwargidan shugaban kasar ta kuma jewa iyalan marigayi dan masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama sule ta’aziyya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  An buɗe tsohon babban birnin Saudiyya domin masu yawon buɗe ido

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *