A cigaba da tallafawa matasa da mata da uwargidan shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari takeyi a fadin kasarnan da ilimin koyon sana’a, taje jihar Kwara inda ta halarci yaye matasa da mata su dubu daya da dari daya da aka koyawa sana’o’in dogaro da kai karkashin gidauniyar ta me suna Future Assured.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A jawabin da tayi a gurin taron, uwargidan shugaban kasar ta bayyana godiyarta ga matar gwamnan jihar kwarar data dauki nauyin ciyar da matasan da suka koyi sana’o’in tun daga randa suka fara har zuwa gamawa, haka kuma ta godewa gwamna Abdulfatah Ahmad na jihar bisa tallafin jari daya baiwa matsan da suka fi nuna kwazo a wajan koyan sana’o’in da kuma gonaki daya baiwa wadanda suka koyi harkar noma, tayi kira ga wadanda suka koyi sana’o’in dasu yi kokarin ganin sun kafu da kawunansu dan talkafawa kansu da kuma iyalansu.
Shima da yake jawabi a gurin taron, gwamna Abdulfatah ya godewa uwargidan shugaban kasar data saka jiharshi ta kwara cikin jihohin da suka karu da wannan koyar da sana’o’i nata, haka kuma gwamnan ya mikamata wani zane da aka mata na musamman.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});