Tsohon tauraron dan wasan kasar Ivory daya taka leda a kungiyar Chelsea, Didier Drogba ya bayyana cewa dan wasan Najeriya Oshimhen zai iya zama zakaran duniya a gasar tamola.
Drogba yace dan wasan mai shekaru 23 dake taka leda a Napoli zai iya zama zakaran gwaji a harkar tamola nan gaba kadan.
Osimhen yayi nasarar ciwa Napoli kwallaye 14 kuma ya taimaka wurin cin biyar a kakar bara.