fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Wa ya kashe kaninsa, yayin da ya kamashi yana Zina da matarsa(Turmi da Tabarya) a Abuja

Lamarin ya farune a unguwar Kubwa dake babban birnin tarayya, Abuja.

 

A daren ranar Larabane, Abdullahi Yusuf ya kama kanin nasa yana masa cin amana da matarsa.

 

Aikuwa bai yi wata-wata ba, ya dauko wuka ya caka masa.

 

An dai kama Abdullahi Yusuf, ya kuma shaidawa manema labarai cewa, matar tasa tace zata je makwabta wamda daga canne sai kanin nasa ya bita gidan makwabtan.

 

Da ya ji shiru shine ya bi sahu, ai kuwa yana zuwa ya shiga dakin da matar tasa take, sai ya gansu tsirara suna lalata.

 

Wani shaida, Olugbenga John, yace bayan da Abdullahi Yusuf ya kashe dan uwansa, ya so tserewa amma suka kamashi suka kira ‘yansanda.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.