fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Wa’azin Malaman Izala a kasashen Turai:”Shin wai meyasa suke saka kananan kayane?”>>inji wasu

Shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau da sakataren kungiyar Sheikh Kabir Gombe suna can kasashen Turai inda suke wa’azi dan daukaka kalmar Allah, Malaman sun fara da kasar Ingila inda daga baya kuma rahotanni suka nuna cewa sun wuce zuwa kasashen Greece da Jamus.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A jiyane aka samu rahotannin yin wa’azinsu a kasar Jamus a cikin wani masallaci da jama’a da dama suka taru dan saurarar wa’azin.

Tun bayan saukarsu kasar Ingila, an rika ganin hotunan malaman sanye da kaya irin na mutanen kasashen turai, wannan bai rasa nasaba da yanayin sanyi dake can da kuma dai kalmarnan da ake cewa “idan kaje gari kaga kowa da bindi, to ko na tsummane kaima kayi kokari ka dasa” da kuma watakila ra’ayi.
Wasu dai sun fara tambayar dalilin da ya saka shuwagabannin Izalan sa kananan kaya, alhalin sarakunanmu na Arewa, kai harma da shugaban kasa, Muhammadu Buhari lokuta da dama idan suka fita kasar waje zaka gansu da kaya irin na Hausawa.
An dai rika mayarwa da irin wadannan mutanen martanin cewa, ai saka kayan hausa, al’adanane ba addiniba.
Munaiwa Malaman fatan Allah yasa su gama abinda ya kaisu su dawo gida lafiya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *