fbpx
Monday, March 1
Shadow

Wace doka ce ta baiwa makiyaya damar daukar AK-47? – Gwamna Ortom ya gayawa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom ya nuna bacin ransa game da kalaman da takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi, wanda ya zarge shi da abin da ya kira “mummunan ra’ayi game da Fulani makiyaya”.

A ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairu, Gwamna Mohammed a wani taro ya zargi Gwamna Ortom da rashin hakuri da sauran kabilu a jiharsa sannan kuma yana kokarin bata wa kabilar Fulani Suna. Ya kara da cewa Fulani makiyaya na dauke da bindigogin AK-47 don kare kansu tunda gwamnati ba ta kare su.

Da yake marya da martani, Gwamna Samuel Ortom, yace yayi matukar mamaki irin yanda takwaran nasa yake zargin sa akan nuna kiyaye ga Fulani makiyaya.

Yace Gwamna Bala Mohammed bai yi masa adalci domin kuwa a cikin Jiharsa akwai Fulani da sauran kabilu yawa dake zaune lafiya saboda da bin doka da oda.

A karshe Gwamna Ortom yayi tambaya ga Gwamna Bala Mohammed ko akwai dokar Nageriya da ta baiwa makiyaya izinin mallakar AK-47?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *