Tsohon Limamin Masallacin Apo dake rukunin gidajen ‘yan majalisun tarayya a babban birnin tarayya, Abuja, Sheikh Nura Khalid ya bayyana cewa, wanda suka dakatar dashi suna nuna alamar suna jin dadin abinda ‘yan Bindiga suke yi.
Ya bayyana hakane a jaridar Vanguard yayin wata ganawa da suka yi dashi.
Sheikh Nura Khalid yana amsa tambaya ne inda aka tambayeshi shin yana ganin abinda kwamitin suka yi na dakatar dashi basu kyauta ba?
Yace bai so yace basu kyauta ba, saboda watakila wasu zasu iya fahimtar cewa, yana son ya koma masallacinne.
Yace amma matakin kusan mutum daya ne ya daukeshi ba wai duka ‘yan kwamitin masallacinne suka cimma matsaya akan dakatar dashi ba.
Yace Sanat Dansadau wanda ya fito daga jihar Zamfara da wani mutum ne suka dauki wannan mataki.
Yace kuma a matsayinsa na wanda ya fito daga jihar Zamfara, Sanatan na nuna alamar cewa, yana goyon bayan abinda ‘yan Bindigar ke aikatawa kenan.
By their action, especially that of the committee chairman who hails from Zamfara, they are sending wrong signals to Zamfara people that they are happy with what the bandits are doing. But you can’t say you sack me, because I said let’s have a united Nigeria free from banditry, crime, terrorism, conflict and insecurity. I am asking for a secured Nigeria. Is that an abomination or a sin?