fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Wadanda suka raba Najeriya da bakin su ne yanzu ke zargin Shugaba Buhari – Femi Adesina ya mayarwa Bishop Kukah martani

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya maida martani ga Bishop na darikar Katolika na Sokoto, wanda ya zargi gwamnatin Buhari da raba kan ‘yan Najeriya ta hanyar kabilanci da addini.

LIB ta ruwaito a baya cewa Kukah ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya gabatar da sakon Ista a ranar 17 ga Afrilu. Ya kuma gargadi malaman addini da su guji fadawa tarkon ‘yan siyasa ta hanyar neman kudi, ya kuma kara da cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na cikin kwanciyar hankali yayin da kasar nan ke cikin mawuyacin hankali.

Karanta wannan  Tura ta kai bango: kalli bidiyon yanda 'yan Inyamurai suka fara kama 'yan IPOB suna kashewa

Ya kuma yi tir da cewa kawai abin da ke aiki a kasar nan shi ne cin hanci da rashawa, ya kara da cewa dole ne a kwato Najeriya daga fadawa cikin halin rashin tabbas.

Da yake mayar da martani kan hakan, Adesina ya wanke shugaban nasa daga duk wani zargi, inda ya dage cewa masu irin wadannan ikirari su ne wadanda suka raba Najeriya da bakinsu, da munanan maganganu ba tare da kariya ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.