Kungiyar ma’aikatan man fetur ta NUPENG ta bayyana cewa, wahalar man fetur da akw ciki ba zata kare ba nan kusa.
Kungiyar ta kuma kara da cewa, Najariya ba zata amfana da irin amfanin da kasashe masu samar da man fetur ke amfana dashi ba na saukin man saboda ta kasa iya tace man fetur dinta a cikin gida, saidai a shigo dashi daga kasat waje.
Shugaban kungiyar, Prince William Akporeha ne ya bayyana haka inda ya caccaki manyan mutanen yankin Naija Delta saboda kasa bude matatun man fetur din da zasu rika tace man a cikin gida Najariya.
Yace da gangan gwamnati ta zabi ta rika shigo da man fetur din daga kasar wajw maimakon ta samar da matatun taceshi a cikin gida.