fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Wahalar ta yi yawa>>TUC ta baiwa shugaba Buhari kwanaki 7 ya janye karin farashin mai ko ta fara yajin aiki

Kungiyar kwadago ta TUC ta bayyana cewa tana Allah wadai da karin kudin man Fetur da na wutar Lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.

 

Kungiyar bayan zaman ganawa da ta yi, ta fitar da sanarwa ta hannun shugabanta, Quadri Olaleye da Sakatarenta Musa Lawal inda tace ta baiwa gwamnati kwanaki 7 ta janye wannan karin kudi.

Tace rashin yin hakan zai kai ga ta tsunduma zanga-zanga da yajin aiki wanda babu ranar dainawa. Kungiyar ta koka da rashawa da cin hanci a ma’aikatun gwamnati irin su NDDC da kuma rashin fara amfani da mafi karancin Albashi na Naira Dubu 30 da wasu ma’aikatu ke yi da dai sauransu.

 

Hakanan kungiyar tace ya kamata a tausayawa masu karamin karfi a cikin al’umma dan wahalar da ake ciki ta yi yawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *