Rahotanni sun watsu sosai inda gidajen jaridun kasashen yamma suka watsa cewa garin Wekan na kasar Oman Azumin awanni 3 kawai suke.
Saidai shin hakan gaskiyane?
Dan tabbatar da hakan wasu sun tashi takanas suka tafi garin na Wekan dan ganewa idanunsu wannan abin mamakin.
Kafar the Times of Oman ta ruwaito wanda suka je garin Wekan sun samu wani tsoho dan shekaru 72 me suna Saif Abdul Al Riyami.
Koda suka tambayeshi gaskiyar labarin da suka ji, sai yayi murmushi.
Yace Azumia garinsu daya yake da Azumi a kowane gari, suma sun ji wancan labarin karyar da ake yadawa.
Yace Rana idan ta fito a garinsu bata dadewa take bacewa, amma bawai faduwa take ba, yace garin nasu na da dogayen duwatsu, idan ranar ta fito, bayan duwatsun take shigewa ta boye sai kuma gobe.
Hakan na faruwane tun daga watan Fabrairu har zuwa Nuwamban kowace shekara.
Yace to shi kuma Azumi ba da ganin rana ake yinsa ba, ana yinsa ne daga hudowar Alfijir zuwa faduwar rana.
Garin dai na da sanyi wanda ke da karfin 30 degree Celsius.