fbpx
Monday, December 5
Shadow

Wai ina Jiragen yakin da aka siyo, me yasa ba za’a yi amfani dasu a kashe ‘yan Bindiga ba>>Tsohon janar din soja ya tambayi gwamnatin tarayya

Wani tsohon janar din sojan Najeriya, John Sura ya bayyana cewa basu jin dadin yanda ake kashe sojojin Najeriya.

 

Wani rahoto ya nuna cewa sojoji sama da 700 ne suka rasa rayukansu a yaki da ‘yan ta’adda. Inda a cikin shekarar da muke sama da 70 ne aka kashe, banda farar hula.

 

Janar John Sura yace akwai karancin kayan aiki na zamani a hannun sojojin wanda kuma ya kamata gwamnatin tarayya ta samarwa sojojin kayan aikin zamani.

 

Yace maganar gaskiya itace sojojin ma na matukar kokari, duk da yaks basu da isassun kayan aiki amma suna yaki da ‘yan ta’addar iya karfinsu.

 

Yace sam basa jin dadi yanda ake ganin cewa sojojin sun gaza wajan samar da tsaro. Yace matsalar tsaro na neman lakume kasar.

Karanta wannan  Da Duminsa: Kungiyar Al-Nasr ta kammala sayen Cristiano Ronaldo akan Miliyan £173

 

A hirar da Punch ta yi dashi yace shin wai ina jiragen yakin da aka siyo na A29 Super Tucano, me zaisa ba za’a yi amfani dasu ba wajan yakar wadannan ‘yan Bindigar?

 

Yace kuma sojoji kadai ba zasu iya yakar wadannan ‘yan Bindigar ba, dole sai an hada da taimakon juna tsakaninsu da sauran jami’an tsaro irin su DSS.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *