fbpx
Thursday, February 9
Shadow

WAIWAYE: Dattijo Dan Shekara 88 Da Ya Shiga Makarantar Firamare

WAIWAYE: Dattijo Dan Shekara 88 Da Ya Shiga Makarantar Firamare

Hotunan Abubakar Muhammad Barinjimi dalibi dan shekara 88 ya dauki hankulan abokan karatunsa da sauran jama’a, yayin da ya shiga aji a makarantar Firamare ta Model ta Hadin Gwiwar Najeriya da Masar da ke Kano, (Nigeria-Egyptian Model School).

Muhammad Barinjimi talaka ne amma yana da kyawawan buri don neman ilimi yayin da yake kusantar shekaru ɗari.

Burinsa dai shine ya yi digiri na uku a ilimin tauhidi.

Dalibai ’Yan uwansa da ke wannan makaranta yawancinsu ‘yan shekara bakwai ne.

Karanta wannan  INEC Ta Fara Horas Da Ma'aikatan Wucin-gadi Milyan 1.2 Domin Aikin Zaɓen 2023

Dattijon dai ya shiga makarantar ne shekaru uku da suka gabata, inda a lokacin ne aka dauki hotunan.

Daga Saliadeen Sicey

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *