Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce “wajibi ne a kawo ƙarshen kashe-kashe” a kasuwar Sasa ta Jihar Oyo.
Atiku na wannan batu ne bayan kashe Hausawa aƙalla 10 a kasuwar da ke birnin Ibadan na JIhar Oyo a rikicin ƙabilanci tsakaninsu da Yarabawa a ƙarshen mako.
“Garin haihuwa na kowane ɗan Najeriya shi ne Najeriya. Najeriya ce ta haifar da garuruwan ba su ne suka haife ta ba. Kowace jiha a Najeriya wajibi ne ta zama ‘yar Najeriya a kodayaushe,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa “saboda haka dole ne a dakatar da zubar da jini a Sasa da ko’ina”.
Rahotanni sun ce wani Bayarabe ɗaya ya ransa a rikicin, wanda ya samo asali daga wani ɗan dako Bahaushe da ya zubar da kayan da yake turawa a baro a gaban shagon wata Bayarabiya.