fbpx
Saturday, August 20
Shadow

“Wallahi Aure Nake So, Na Gaji Da Kwana Ni Kaɗai”. Cewar Wata Budurwa Dake Neman Miji Ruwa-Ajallo

Daga Zaharaddeen Gandu

Wata kyakkyawar budurwa ta koka, kan yadda take matuƙar son aure amma babu wanda ya fito, ta ɗauki takaitaccen bidiyo ta wallafa a shafinta tana kukan takaicin rashin mijin aure.

A wani bidiyo da jaridar Labarun Hausa ta ci karo da shi dake yawo a shafukan sadarwa, ya nuna yadda wata budurwa ke rusa kuka tana bayyana irin yadda take son aure.

Bidiyon mai tsawon daƙiƙa 15 ya nuno budurwar mai suna dinaouma1 a shafin tiktok cikin hijabi tana kuka tana cewa:

“Wallahi aure nake so, na gaji da kwana ni kadai”.

Wannan bidiyo ya ɗauki hankula da yawa inda mutane da dama suka dinga yadawa a shafukansu, a cikin mutanen da suka wallafa wannan bidiyo a shafikansu na sadarwa akwai, tsohon Sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani. Sai kuma wani mai suna Muhammad T. Shehu, wanda ya wallafa yayi rubutu a kasa kamar haka:

“Jama’a dan Allah a samu wani ya auri wannan baiwar Allah mana.”.

Karanta wannan  Labari me dadi: An kwato buhunan takin zamani da 'yan ta'adda suka siya dan hada bamabamai

Kamar yadda kowa ya sani yanzu mun shigo wani zamani da rayuwa tayi wahala, haka abubuwa na addini da al’ada na cigaba da canja wa a kowacce rana, hakan ya sanya al’umma da dama ke shiga cikin wani hali idan suka buƙaci wani abu da zai sanya su jin daɗin rayuwa suka rasa.

Samari da ‘yan mata da yawa a wannan zamani na bukatar aure, sai dai kuma wasu dalilai da dama na hana su ganin sun cimma burinsu.

Budurwa na neman aure a lokuta da dama, samari na samun matsalar aure sakamakon rashin aikin yi, rashin kuɗi da sauran su, yayin da su kuma mata a nasu ɓangaren sukan samu matsala sakamakon rashin hali, wasu kuma saboda ruwan ido da wani buri na abin duniya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.