fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Wallahi na rantse da Allah ban taba goyon Tinubu ya zabe ni a matsayin abomin takararsa ba, cewar Kashim Shettima

A jiya dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zabe mai zuwa.

Wanda shugaban APC Abdullahi Adamu ya halatta, Kashim Shettima yayi bayanai bayan an kammala kaddamar dashi a matsayin abokin takarar Tinubu.

Inda sanatan jihar Bornon yace shi bai yadda aka bashi wannan mukamin don ya nuna goyon baya ga hausawa da Kanuri ba.

Kuma wallahi tallahi shi bai taba cewa Tinubu ko kuma ya nuna goyon bayan ya zabe shi ba a matsayin abokin takararsa na zabe mai zuwa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.