‘Yan Bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasar dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja sun saki sabon bidiyo.
Daily Trust ta bayyana cewa, ta ga bidiyon kuma a cikinsa sun zane sauran fasinjojin dake hannunsu.
Sannan sun sha Alwashin kama shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai su kashe.
Hakanan sun sha alwashin tarwatsa Najariya.