fbpx
Monday, June 27
Shadow

Wane Dan Takara Arewa Za Ta Goyawa Baya?

A gobe ne ake saka ran babbar jam’iyyar adawa ta PDP zatayi zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugabancin ƙasa. Ana saka ran jam’iyyar ta PDP zata fitar da dan takarar ta ne daga yankin Arewa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da tsohon shugaban majalisar Dattijai sune yan takara mafi samun rinjaya da goyon baya. Kowannen su yana da kwarewar aiki da jimawa a cikin tsarin mulki da siyasa.

Wanene ya Kamata Arewa ta goyawa baya?

Alh Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa. Shine mafi dacewar samun goyon bayan arewa. Saboda kwarewar sa a fannin kasuwanci, tsaro, ilimi, samar da aikin yi, siyasa da sauran fannukan rayuwa. Alh Atiku Abubakar ba sabon mutum bane a wajen yan Najeriya, baya bukatar sabon talla kamar sauran abokan karawar sa.

Karanta wannan  Hukumar zabe zata karawa 'yan Najeriya lokaci don su cigaba da rigistar katin zabe, cewar Mahmood Yakubu

Atiku Abubakar ya samar da aikin yi tare da taimakon addini fiye da kowanne a cikin mutum 5 da suke takara daga arewa.

A yanzu dai ana dakon jiran gobe Asabar don ganin yadda zata kaya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.