fbpx
Monday, August 8
Shadow

Wani Abin mamaki akan Buhari da sai Mumini Masoyin Manzon Allah(SAW) za’a samu da irinshi>>General BMB

Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello ya bayyana cewa akwai wani abu da yasa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya zama dan baiwa wanda kuma samun irinshi na da matular wuya, saboda sai Mumini, Masoyin Manzon Allah (SAW) ake samu da irin wannan abu.

 

Bello ya bayyana hakane ta shafinsa na Instagram inda yace makiya fa saidai su yi hakuri akan shugaban kasar.

Ga abinda Bello ya rubuta kamar haka:

 

“(WANI ABIN AL’AJABI KAN PMB)

Da iyayen shugaba Muhammadu Buhari suka haifeshi, lokacin yana kwana bakwai a duniya, yana jinjiri bare ya zabi sunan da yake so a rada mishi.

Aka rada mishi suna (MUHAMMADU)
Allah ya hadashi aure da (AISHA)
Allah ya bashi ‘ya mai suna (FATIMA)

Idan ba Mumini ba, masoyin Manzon Allah, zaiyi matukar wuya mutum ya samu irin haka!

Ka samu sunan fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW),
ka samu mata mai sunan matar Annabi Muhammadu (RTA)
Ka haifi diya mai sunan ‘yar Annabi Muhammadu (RTA)

WALLAHI SHUGABA MUHAMMADU BUHARI BAWAN ALLAH NE KUMA ‘DAN BAIWA.
Sai dai makiyya suyita hassada amma mai neman kahon kare ya wahala. Kawai ku barshi sai ta Allah ba ta mutum ba.

ALLAH YA KARA LAFIYA BABA.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.