fbpx
Monday, March 1
Shadow

Wasu Sarakunan Gargajiya sun ce Sojoji na hada kai da mahara

Waau sarakunan gargajiya a Ketuh dake jihar Ogun ya jawo hankalim hukumar sojin Najeriya inda suka yi zargin cewa waau daga cikin sojojin na hada kai da fulani makiyaya ana kai musu hari.

 

Sarakunan da suka yi wannan zargi sune, Oba Michael Dosumu, Oba Akintunde Akinyemi, da Kuma Oba Gabriel Olalowo.

 

Sarakunan sun aikewa kwamandan sojojin Abeokuta wasika inda suka yi zargin cewa sojojin sun raka Filani makiyaya inda suka kaiwa al’ummarsu hari. Sun ce lamarin ya farune ranar 19 ga watan Disamba.

 

A cikin wasikar da suka aikewa Kwamandan sojin sun yi zargin cewa sojojin sun ke wani kauye a yankinsu inda suka gayawa mutanen kauyen cewa Fulani zasu je da dabbobinsu su yi kiwo, bayan jawabinsu, sun nemi idan akwai me tambaya, wani Seye Mulero ya tashi yana gaya musu illar zuwan Fulani kiwo a kauyen nasu inda yace ana samun kashe-kashe kuma suna lalata musu amfanin Gona. Saidai Sarakunan sun ce dalilin wannan kalami,  Sojojin sun kama Seye suka masa dukan tsiya.

 

Sun kuma zarce zuwa wani kauyen inda al’ummar kauyen suka ki amincewa anan ma an nemi cin zarafin wasu.

 

Sarakunan sun nemi da cewa a binciki sojojin da suka kai wadannan hare-haren dan hukuntasu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *