Wani dalibin dake shekarar karshe ta karatun kiwon lafiya a kasar Ukraine ya mutu makonni biyu bayan ya dawo gida Najeriya.
Dalibin mai suna Uzaifa Halilu Modachi ya kasance daya daga cikin yan kasar Najeriya aka dawo dasu a kwanakin da suka gabata daga Ukraine, kuma an binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Mahaifin dalibin wanda ya kasance da mahalisar wakilai a jihar Sokoto Habibu Haliru Modachi ya bayyana cewa haka Allah yake ikonsa ya kan dauke rayuka a kowane lokaci, kuma suna godiya ga gwamnatin Sokoto akan kokarin datayi na dawo da su daga Ukaraine.