Wani dalibin kwalejin kimiyya ta Polytechnic a jihar Imo dan shekara 20, Izu Nnawuihe ya kashe kansa da kansa ta hanyar rataya a bayin gidansu.
Augistine ne ya bayar da wannan labarin inda yace mamacin na tare da mahaifiyarsa da ‘yar uwarsa ne suna tsaka da hira kawai sai yace masu zai je bayi.
Wanda bayan tafiyar tas ne aka kira shi a waya sai ‘yar uwar tasa taje kai masa inda ta ganshi ya rataya kansa ya mutu.
Wanda hakan yasa ta kirawo mahaifiyar tata har suka nemi dauki wurin al’umma.