
Wani dan kasar Sweden me suna Martin Strid yayiwa Fiyayyen halitta, manzon tsira, Annabu Muhammadu (S.A.W) batanci da dukkan musulmin Duniya baki daya, shi wannan la’ananne yayi wata magane a lokacin da yake wani jawabi a gurin babban taron jam’iyyarshi ta Sweden Democrat, SD a takaice, ya bayar da misalin wani ma’auni inda yace a jikin ma’aunin akwai maki 100 zuwa 1.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Yaci gaba da cewa inda maki dari yake to nan ne cikakkun mutane suke inda kuwa maki daya yake to nanne muhammaden(watau mabiya addinin musulunci) suke.
Yaci gaba da cewa duk musulmai ba cikakkun mutane bane, suna kan wannan wannan ma’auni amma basu kai matsayin cikakkun mutane ba, su kuwa ‘yan kungiyar ISIS suna kusa da zama Muhammaden, watau wadanda ba mutane ba.
Ya kara cewa, idan ka bar addinin musulunci to ka kama hanyar zama cikakken mutum.
Ya kuma ce yana da burin raba musulmai da addinin musulunci, dan su shiga jam’iyyarshi ta SD.
Tun bayan da mutumin yayi wannan kalami, ranar Asabar data gabata, sai ya dauki hankulan Mutane.
Jam’iyyar tashi ta Sweden Democrat ta nesanta kanta da wannan kalamai da yayi inda ta bayyana kalaman na Strid a matsayin wadanda suke nuna banbancin launin fata. Kuma sun bayyana cewa duk mutum mutumne, ko da kuwa daga wace irin kabila ya fito a Duniya, haka kuma sunce sun fara zaman shawara akan korar Strid daga jam’iyyar tasu.
Shima dai Strid ranar Lahadi yayi nadama, inda yace wai ayi hakuri, yana da abokai musulmai, kuma yana girmamasu, subutar bakine tasa ya fada haka, kuma lokacin yana cikin gaggawane, kuma idan mutum yayi abu yana gaggawa to zai iya yinshi ba daidaiba.
Kafafen watsa labarai na The local ta kasar Sweden din da kuma RT ta kasar rasha duk sun ruwaito wannan labari.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});