fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Wani Dankasuwa A Kasar Indiya ya siyi Tukunkumin rufe hanci na Zinare akan kudi Dala $4’000

A yayin da Duniya ke ci gaba da gwagwarmayar yaki da cutar Korona, abu daya da yazama dole shine sanya takunkumin rufe hanci domin samun kariya daga kamuwa da cutar wadda a kai imanin na da saurin yaduwa cikin al’umma.

Kasancewar sanya takunkumi shine abu mafi mahimmanci da Duniya ta yadda ko ta amince da yin amfani dashi domin kaucewa yaduwar ko yada cutar coronavirus cikin jam’a.

Tayu haka ne ya sanya wani Dan kasuwa Dan kasar India mai suna Shankar Kurhade wanda ke zaune a Pune dake yammacin kasar indiya, Inda ya siyi takunkumin rufe hanci na Zinare mai tsadan gaske domin samun kariya daga cutar Korona Mai saurin yaduwa.

An dai bayyana cewa Dan kasuwan ya siyi takunkumin rufe hanci ne akan kimanin kudi Dalar Amurka Dala $4,000. (1.7 m)

Shankar yayi Imanin cewa sanya takunkumi da sauran matakan kariya zai taimaka mishi wajan samun kariyar kamuwa da cutar Korona.

 

Da yake bada amsar ta yadda yake yin numfashi a lokacin dake sanye da takunkumin zinare ya bayyana cewa “An tsara takunkumin ne da wasu kananan kafofi dake taimaka min in yi Numfashi.

Ya kara da cewa “bani da tabbacin hakan zai iya kare ni daga kamuwa da cutar amma Ina daukan wasu matakan kariya.

Shankar ya zama sananne wajan mutane kasancewar sa na amfani da takunkumin  zinare mai tsadan gaske, hakan ya sanya mutane ke masa kallo a matsayin mai sonkai da kuma kawa.

Ya zuwa yanzu kasar Indiya nada adadin mutum 648,315 da suka harbu da cutar Korona inda aka samu mutuwar mutane 18,655, CGTN Africa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.